Saturday, September 16, 2017

ABINDA YA FARU A MASALLACI.

Bayan an idar da Sallan Magariba sai Malamin ya mike ya fara wa’azi ,ya samu kusan minti 30 yana wa’azi Jama’a suna sauroronshi. Cikin wa’azinsa yana ta fadin falalolin Sahabai da Magana dangane da Bidi’a da shirqa da yan Bidi’a. Sai yace baya fatan har yagama wa’azi ayi sallan Isha ya fita daga Masallacin nan wani bayi masa tambaya ba.
Bayan ya tsaya da wa’azin sai yace babu mai tambaya? Babu mai tambaya? Babu mai tambaya? Dan Allah mai tambaya ya yi.
Sai wani ya daga hannu yace; yana da tambaya. Sai Malamin yace; menene tambayan na ka?.
Sai yace; Malam naji wadannan Yan shi’a sun cewa Sayadatuna Aisha matar Annabi {s} wai kasheta akayi.kuma wai Sayadina Ma’awuyyane ya kasheta. Ina tambayane shi da gaskene kasheta akayi kuma waye ya kasheta? Ma’awuyya ne?
Idan kuma ba kasheta akayi ba, ta rasune ta sanadiyyar rashin lafiya ko wani abu dan Allah Malam a inane kabarinta yake? .
Idan kuma Ma’awuyyane ya kasheta to naji cikin wa’azin Malam yana kiran sunan Ma’awuyya yana cewa Allah ya yarda dashi. Shin wanda yayi kisankai ko ya kasha matan Annabi za’ace Allah yayarda dashi?.
Sai Malam yace; a ina kaji wannan Maganar banzan? sai mutumin yace; ni yanzu tambayanka nakeyi da gaskene haka ta faru?
Sai malamin yace; ai sahabai duk abinda suka aikata mai kyau ko mara kayu Allah ya yafe masu tunda ance duk wadanda sukayi hijira kuma suka taimaki Annabi Allah yayi masu alkawarin Aljanna.
Sai Mutumin yace; to danme ku malaman masamman na Ahalilsunna ku ke cewa; Annabi ma ranar kiyama bai san matsayinshi ba.
Sai Malam yace; ku matsalarku kullun kuna wajen niman kudi bakuyin karatu ba zaku gane ba.
Sai mutumin yace; ko’ kuma kuna fadin ra’ayinku bakuson agane ke nan.
Sai wani dattijo ya mike yace wa malamin kai kace ayi tambaya kuma an samu mai yin tambaya baka bashi amsa ba ka kamashi da fada.
Sai masallaci ya kaure da muhawara , wasu sukace malam ya bada amsan tambayar da akayi masa ko kuma ya daina zuwa masallancin nan.

No comments:

Post a Comment